✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi bikin karrama ma’aikatan Daily Trust da Aminiya

Kamfanin Media Trust Limited, mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya ya karrama ma’aikatan  kamfanin a Abuja. Bikin karramawar, wanda ya wakana a Otel din…

Kamfanin Media Trust Limited, mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya ya karrama ma’aikatan  kamfanin a Abuja.

Bikin karramawar, wanda ya wakana a Otel din Chida da ke Abuja, an shirya shi ne domin karrama ma’aikatan da suka jajirce wajen yi wa kamfanin aiki na sama da shekara goma da wadanda suka kai shekara 15, kuma suka nuna kwazo da gaskiya da rikon amana a tsawon lokacin da suke aikin.

Bikin ya samu halartar daraktoci da manyan jami’an gudanarwa na kamfanin, wanda hakan ya kara kayata taron.

Da yake jawabi a wajen bikin, Babban Jami’in Gudanarwar kamfanin kuma Babban Edita, Malam Mannir dan Ali, ya taya wadanda aka karrama murna, sannan ya ce ya ji dadin yadda ya ga wadanda za a karrama sun zo cikin nishadi tare da iyalansu.

“Ina fata kun zagaya da su domin su gane wa idonsu yadda muke aiki. Ba mamaki wasu daga cikin iyalan wadanda suka zo wannan bikin ko maza ko mata sun dade suna kokawa bisa yadda mazajensu, ko matansu suke dawowa gida bayan ko’ina  an tashi daga aiki. Wasu suna ganin wasu ma’aikata watakila makwabtansu, suna dawowa da yamma, amma sai su ga nasu sai cikin dare suke dawowa.

“To haka ne yanayin aikin yake. Mu aikinmu babu lokacin da ba na aiki ba, kullum ne kuma a kowane lokaci na shekarar baki daya. Don haka ina tawa wadanda aka karrama murna sosai” inji Mannir dan Ali.

Daga cikin wadanda aka karrama a bangaren Aminiya, akwai Edita, Malam Balarabe Ladan da Editan labarai Malam Bashir Yahuza Malumfashi da kuma Malam Abubakar AbdulRahman Dodo.

A bangaren Daily Trust kuma, an karrama Mataimakin Babban Edita, Malam Mahmud Jega da Nathaniel Biban na bangaren Daily Trust ta ranar Asabar, sai mai tsara shafukan Aminiya da sauran jaridun kamfanin, Malam Sani Ahmad da wadansu ma’aikata kusan 30.

Kafin a nade tabarmar taron bikin, sai da Malam Bashir Yahuza Malumfashi ya rera wasu baitoci na musamman domin jinjina ga kamfanin Media Trust da shugabanninsa.

Ga wakar nan mai taken Nasara:

Nasara

Godiya muke wa Allah,

Media Trust ta shilla,

Kominmu babu wahala,

Nasara fa mun same ta.

Shekara guda har goma,

Wasu sha biyar sun tsoma,

An san mu ba mu da homa,

Jarumanmu sun cancanta.

Shugabanni duk sun shana,

Ba dare bare ko rana,

Aikinsu ba ya kwana,

Himmarsu ta bambanta.

Malam Kabiru Babba,

Manniru kai ne Baba,

dan Indiya yau ka tarba,

Kamfanimu ya tabbata.

To sai mu bude hannu,

Addu’a mu yo ta a sannu,

Allah Ya kare jinnu,

Nasara mu samu ta gota.