Wani jami’an dan sanda ya rasa ransa yayin da wasu kuma suka samu raunuka sakamakon wani harin da ’yan ta’addan Boko Haram/ISWAP suka kai wa shingen binciken ababen hawa na jami’an tsaro a kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri.
Rahotanni sun ce an kai harin ne a dab da garin Auno da ke karamar Konduga a Jihar Borno.
- Tukin Babbar Mota Ba Na Matsoraci Ba Ne —Direban Tanka
- Daga karshe Buhari ya saki Dariye da Nyame daga kurkuku
Jin karar harbin bindigar ne ya jawo hankalin sojoji wadanda ba su da nisa da garin na Auno, inda suka rugo suka fatattaki maharan.
Auno na da nisan daga babban birnin jihar Borno mai fama da rikici, kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.
’Yan ta’addan da dama ne dai suka kai hari a kan shingen binciken jami’an ’yan sandan wajen karfe 01:00 na daren Lahadi, inda suka fara harbe-harbe da zuwansu kamar yadda suka saba
Wani jami’in leken asiri ya shaida wa Zagazola Makama, wani kwararre kan yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi cewa jami’an biyu da ke bakin aiki, sun yi artabu da ’yan ta’addan ne da bindiga, wanda ya yi sanadin kashe dan sanda guda daga cikinsu.
Ya ce da jin karar harbe-harbe, sai sauran jami’an suka garzaya wurin da ’yan ta’addan suke domin kai musu dauki.
Ya bayyana cewa ana kyautata zaton ’yan bindigar sun bi hanyarsu ce ta wata hanyar da aka tona, suka kuma kutsa cikin wurin da kafa, kafin su kai hari ga shingen jami’an tsaron.
Wannan yanki na Auno dai yanki ne da ya rika fama da hare-haren mayakan na Boko Haram/ISWAP a baya, wadda ya kai ga hatta mazauna garin sai da suka tarwatse daga bisani gwamna Babagana Umara Zulum ya sake tsugunar da su.