Sabbin kuratan soji 6,400 ne aka yaye daga Makarantar Horas da Kuratan Soji ta Kasa da ke garin Zariya a Jihar Kaduna.
Da yake jawabi yayin bikin yaye sabbin sojojin karo na 80, Kwamandan Runduna ta 1 da ke Kaduna, Manjo-Janar Danjuma Ali Keffi, ya hori sabbin sojojin da su kasance masu aiki tukuru don ci gaban kasa.
Ya nemi da su yi amfani da kwarewar da suka samu wurin tunkarar kalubale na matsalar tsaro da kasar nan take fuskanta.
A cewarsa, “A iya sani na,daukacin sabbin sojojin sun samu horo da kwarewa mai inganci lokacin da ake horas da su, kuma ina fatan za su ci gaba da kasancewa masu amfani da horon da suka samu ta fannin aikin soji a wannan kasa.”
Ya hore su a kan zama ’yan kasa na gari tare da kiyaye martaba da kai’dar aikin akin soja da dokokin kasar.
Bako mai jawabi ya kuma yi wa Babban Hafsan Sojin Kasa Manjo-Janar Ibrahim Attahiru da Allah Ya yi wa rasuwa addu’ar samun Rahamar Ubangiji da sauran ’yan tawagarsa da suka riga mu gidan gaskiya.
Bayan kammala bikin yaye sabbin kuratan Manjo-Janar Ali Keffi ya kuma kaddamar da sabuwar Cibiyar Kiwon Lafiya da aka gina a makarantar horas da kuratan.