Wata babbar kotun jihar da ke zamanta a Ado-Ekiti babban birnin jihar Ekiti a ranar Laraba ta yankewa wasu mutane biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda fashi da makami.
Wadanda aka yankewa hukuncin, Lanre Kayode mai shekaru 34 da Olanrewaju Aremu mai shekaru 35, wadanda suke dauke da bindigogi da adduna, sun yi wa wata mata mai suna Oluremi Jimoh fashin na’ura mai kwakwalwa, wayoyi da mota kirar Toyota Camry.
Hukuncin dai ya zo ne kasa da mako guda bayan da wata Babbar Kotun Jihar ta yanke wa wasu maza biyu hukuncin kisa kan irin makamancin wannan laifin.
Da yake yanke hukunci, alkalin kotun, mai shari’a Lucas Ogundana ya ce, hukuncin ya yi daidai da tanadin doka kan duk wanda aka tabbatar ya aikata laifin.
Tun da farko dai an tuhumi mutane biyun ne da amfani da bindigogi da adduna don yi wa wata mata mai suna Jimoh Folajoke Oluremi fashin kayan da suka hada da na’ura mai kwakwalwa da wayoyi da kuma motar a ranar 14 ga watan Yulin 2017, da misalin karfe biyu na dare a unguwar Oke-Ila dake Ado-Ikiti,
Matar ta shaidawa kotun cewa an kama wadanda ake zargin ne bayan yan sanda sun bibiyi wayoyinta bayan aikata fashin, wanda hakan ya sa aka kwato sauran kayayyakin.
Tun da farko dai Babban Mai Shigar da Kara na jihar Olawale Fapohunda ne ya shigar da karar ya kuma gabatar da shaidu hudu, kafin daga bisani su ma wadanda ake zargin su amsa aikata laifin da kansu.