✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yanke wa shugaban kulob din AC Milan Silbio Berlusconi hukuncin shekara bakwai

A ranar Talata da ta wuce ne wata kotu a kasar Italiya ta yanke wa tsohon Firaministan Italiya kuma Shugaban kulob din AC Milan Silbio…

A ranar Talata da ta wuce ne wata kotu a kasar Italiya ta yanke wa tsohon Firaministan Italiya kuma Shugaban kulob din AC Milan Silbio Berlusconi hukuncin daurin shekara bakwai a gidan maza.
Kotun ta ce ta same shi da laifi ne a bisa tuhumar da ake masa na yaudarar wata budurwa ’yar kimanin shekara 17 da kudi kuma ya yi lalata da ita a lokacin da yake rike da mukamin Firaminista.
Budurwar, mai suna Karima El Mahroug an ce Berlusconi ya yi amfani da ba ta makudan kudi ne sannan yin lalata da ita a wani otal a lokacin da yake rike da mukamin Firaminista.
Sannan kotun ta kara da cewa ta samu Berlusconi da laifin yin  amfani da karfin iko a matsayinsa na Firaminista a wancan lokaci wajen kubutar da ita daga jami’an tsaro na ’yan sanda a lokacin da ake tuhumarta da laifin sata.
Kotun ta ce an yanke masa hukunci daga yanzu har zuwa tsawon rayuwarsa cewa ba ta amince wa dattijon dan kimanin shekara 76 rike kowane irin mukami a kasar ba saboda laifuffukan da ya aikata.
Sai dai rahoton da kafar sadarwar soccernet.com ta kalato ya nuna Berlusconi yana da damar daukaka kara don kalubalantar wannan hukunci.
Lauyan da ke kare Silbio Berlusconi mai suna Niccolo Ghedini ya bayyana hukuncin a matsayin “almara” kuma ya sha alwashin daukaka kara don kalubalantar hukuncin.