Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta yanke wa Faisal, dan tsohon Shugaban Kwamitin Gyaran Fansho ta Kasa (PRTT), Abdulrasheed Maina, hukuncin daurin shekara 24 a gidan yari.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Okon Abang, da yake yanke hukuncin, ya ce kotun da samu Faisal da laifuka uku da ake tuhumar sa da aikatawa.
- Yadda aka tsaurara tsaro a Majalisa kafin mika kasafin 2022
- Africa Magic zai yi fim a kan Aisha Buhari
Alkalin ya yanke masa hukuncin shekara biyar kan laifin farko da aka same shi da shi, sannan kuma aka sake yanke masa hukuncin shekara 14 ga laifi na biyu da ake tuhumar sa.
Kazalika, alkalin ya umarci da a tisa keyar dan Abdulrasheed Maina zuwa gidan yari nan take.
Idan ba a manta ba, an gurfanar da Faisal tare da mahaifinsa Maina a gaban kotu, kan zargin sama da fadi da wasu kudade.
Amma tun a wancan lokaci Faisal ya musanta zargin da ake masa a gaban kotu.
EFCC ta cafke Faisal tun a ranar 25 ga watan Oktoba 2019, sannan aka ba da belin sa a ranar 26 ga watan Nuwamba 2019 kan Naira miliyan 60, tare da gabatar da wanda zai tsaya masa.
Sai dai, bayan karbar belin sa, sai ya daina halartar zaman kotu tun a watan Satumbar 2020.
Hakan ya sa alkalin kotun ya bukaci da a gabatar masa da Sani Dan-Galadima, dan majalisar tarayya mai wakiltar Kaura-Namoda daga Jihar Zamfara, wanda shi ya tsaya wa Faisal yayin karbar belin.
Har wa yau, alkalin ya sake ba da umarnin cafke Faisal sakamakon kin ci gaba da halartar zaman kotun.
Ya kuma ba da umarnin kwace kadarorin da dan majalisar ya yi amfanin da su wajen karbar belin Faisal.