Kotun Lardin Tsakiya a Kasar Sin da ke zama a Henan, ta yanke wa wata Malamar makarantar kananan yara hukuncin kisa, bayan kama ta da laifin ciyar da dalibai da dama guba a cikin fate.
Malamar wadda ba ta bayyana dalilin aikata ta’asar ba, sai dai ana zargin ta aikata hakan ne domin ta jefa wata abokiyar aikinta cikin matsala bayan samun rashin jituwa a tsakaninsu.
- ’Yan sanda sun cafke mata da miji da kan mutum a Ogun
- Zulum ya gana da iyalan jami’an tsaron da aka kashe a harin Baga
Kotun ta ce, malamar mai suna, Wang Yun, ta zuba sinadarin sodium nitrite ne a cikin faten da aka dafawa daliban ajin abokiyar aikinta, da a sanadiyar haka yara 25 suka kamu da rashin lafiya.
Rahotanni sun bayyana cewa yaran ‘yan tsakanin shekaru 3 zuwa 6 sun yi ta amai har da suma bayan karin kumallon da suka yi da faten, inda daga bisani aka garzaya da su Asibiti.
Sakamakon gubar da ta basu ne yaro daya ya yi ta fama da matsananciyar rashin lafiya ta watanni uku kafin ya mutu a watan Janairun 2020.
Kotun birnin Jiaozuo a ranar Litinin ta ce, Wang ta san sodium nitrite na da illa amma ta zuba musu a abinci ba tare da la’akari da illar da zai haifar ba, saboda haka ta yanke mata hukunci kisa.
Yayin zartar da hukuncin a wannan mako, Kotun ta kuma ce, Wang da Shugaban makarantar za su biya iyayen yaran diyya.
Jami’an tsaro sun ce ba shi karon farko da Wang ta yi amfani da sinadarin sodium nitrite ba a matsayin guba domin ta taba sanya wa mijinta a cikin kofin shayi har ya raunata shi.