Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF), ta ware motocin jigilar magoya bayan tawagar ‘yan wasan Super Eagles, zuwa filin wasa na M.K.O Abiola da ke Abuja, kyauta.
A yammacin ranar Talata ne da misalin karfe 6 na yamma, Najeriya da Ghana za su sake karawa a karo na biyu, a wasan fidda gwanin zuwa gasar kofin duniya da za a yi a kasar Qatar.
- Najeriya da Ghana: Gwamnati ta ba da umarnin rufe ofisoshi da wuri
- NAJERIYA A YAU: Yadda Maye ya cinye Aljan a Babban Taron APC
Kazalika, gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin rufe ofisoshin gwamnatin tarayya da ke birnin tarayya da misalin karfe 1 na rana, don bai wa masu sha’awar zuwa kallon wasan dama.
Tuni tawagar’yan wasan Black Star na Ghana suka iso babban birnin tarayyar Najeriya Abuja, da yammacin ranar Litinin.
A satin da ya gabata Ghana ta karbi bakuncin ‘yan wasan Super Eagles, inda aka ta shi wasan babu ci.
Idan ba a manta ba kasar Ghana ta gaza fitowa daga matakin rukuni a gasar kofin nahiyar Afrika da gudanar a kasar Kamaru, yayin da kuma Najeriya ta fara da kafar dama amma Tunusiya ta yi mata cikas.
Tuni dai masu sharhi kan sha’anin wasanni ke ganin Super Eagles na da damar yin nasarar zuwa gasar kofin duniya, idan ta yi nasara a kan Black Star ta Ghana.