✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ware $3.02bn domin aikin layin dogo daga Maiduguri zuwa Fatakwal

Majalisar Zartarwa ta Kasa ta amince a bayar da kwangilar aikin gyara tare da sabunta layin dogo da ya tashi daga Maiduguri a Jihar Borno…

Majalisar Zartarwa ta Kasa ta amince a bayar da kwangilar aikin gyara tare da sabunta layin dogo da ya tashi daga Maiduguri a Jihar Borno zuwa Fatakwal, Jihar Ribas.

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ne ya sanar da hakan lokacin da yake wa ‘yan jaridar fadar shugaban kasa jawabi kan abinda taron majalisar karo na 18 ta fasahar bidiyo ya tattauna.

Taron dai wanda shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta ya gudana ne a dakin taron fadar shugaban dake Abuja ranar Laraba.

Rotimi ya ce, “A yau Majalisar Zartarwa ta amince a bayar da kwangilar gyarawa da sabunta titin layin dogo daga Maiduguri zuwa Fatakwal da zai hada jihohin gabashin Najeriya mai dauke da sabbin tashoshin sufurin kayayyakin.

“Mun kuma amince a gina tashar jiragen ruwa a Bonny karkashin shirin hadin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu da kuma gina tashar jiragen kasa ta masana’antu a Fatakwal.

“Aikin layin dogon zai lashe $3,020,279,549. Shi kuma aikin tashar masana’antun, wanda gwamnati ba za ta kashe ko sisin kwabo ba za a yi shi a kan $241,154,389.31.

“Wannan aikin na Maiduguri zuwa Fatakwal zai samar da sabbin tashoshi; daga Fatakwal zuwa Bonny da kuma daga Fatakwal zuwa Owerri.

“Kazalika, za a samar da wani layin da zai dangana da garin Kafanchan.

“Akwai wata tashar daga Gombe, kafin a kai Maiduguri zuwa Damaturu da Gashuwa. Wadannan sune ayyukan da aka amince dasu,’’ inji ministan.