✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An wanke Adesina daga zargin rashawa a bankin Afirka

Kwamiti mai zaman kansa da ya kara bincikar Shugaban Bankin Raya Afirka (AfDB), Akinwumi Adesina, ya wanke shi daga zarge-zargen da yake fuskanta. Adesina ya…

Kwamiti mai zaman kansa da ya kara bincikar Shugaban Bankin Raya Afirka (AfDB), Akinwumi Adesina, ya wanke shi daga zarge-zargen da yake fuskanta.

Adesina ya fuskanci zargi 16 da wasu masu alaka da cin hanci da bai wa ‘yan uwansa manyan mukamai da kuma bayar da kwangiloli ga ‘yan uwa da abokansa.

Tun da farko wani kwamiti ya wanke Adesina, bayan ya yi bincike kan zargin bai same shi da laifi ba.

Daga baya kasar Amurka ta huro wuta a kan cewa dole sai an kara wani binciken.

Sabon kwamitin da Tsohuwar Shugabar Kasar Ireland, Mary Robinson ta shugabanta ya tsaya kan hukunci da aka riga aka yanke a rahoton da ya fitar cewa: “Mun aminta da hukumcin da kwamitin da’a ya yanke kan zarge-zargen da aka yi wa Shugaban AfDB. An yi adalci, kuma yin watsi da zarge-zargen ya yi daidai”.

Rahoton kwamitin da ya wanke Adesina ya bai wa gwamnonin bankin damar kara zabar sa a zaben da ke tafe daga ranar 25 zuwa 27 ga watan Augusta.

Zaben zai ba Adesina damar ci gaba da mulkin Banki na wasu shekaru biyar a karo na biyu.

Tuni ‘yan Majalissar Tarayya da Ministan Masana’antu suka mara masa baya ya yi takarar karo na biyu.

’Yan kwamitin da ya wanke Mista Adesina sun hada da Ministan Shari’ar Gambiya Hassan Jallow da Leonard McCarthy, wanda shi ne Mataimakin Shugaban Sashen Tsare Gaskiya na Bankin Duniya.