Gwamnatin Taliban ta kasar Afghanistan ta tura ’yan kwaya 3,500 cibiyar gyaran hali don ceto su daga halin da suka fada.
Daraktan Hukumar yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi ta kasar, Hayatullah Rouhani ya bayyana a ranar Alhamis cewa, kimanin mutum 50 sun mutu a cikin wata biyun da suka shude sakamakon ta’ammali da miyagun kwayoyi.
“Bayan tabbatar da an raba su da shaye-shayen, za a sake mika su ga ’yan uwansu,” in ji Rouhani.
Rahotanni daga kasar sun ce a watan Afrilun bara gwamnatin kasar karkashin Taliban ta haramta nomawa da kuma sarrafa miyagun kwayoyi a fadin kasar.
Tun daga wannan lokaci gwamnatin ta yi damara da yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi a kasar.