✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tura tubabben Sarkin Kano zaman hijira a Jihar Nasarawa

An tura tubabben Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II zuwa zaman hijira a Jihar Nasarawa. Jaridar Intanet ta Daily Sun ce ta bayyana haka, inda ta…

An tura tubabben Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II zuwa zaman hijira a Jihar Nasarawa.

Jaridar Intanet ta Daily Sun ce ta bayyana haka, inda ta ce wasu majiyoyin Majalisar Masarautar Kano sun shaida mata cewa an fice da tsohon Sarkin daga fadar, kuma wadansu jami’an gwamnati da jami’an tsaro ne suka yi masa rakiya zuwa filin jirgin sama a hanyarsa ta zuwa Jihar Nasarawa.

A safiyar yau ce Gwamnatin Jihar Kano a karkashin Gwamna Abdullahi Ganduje ta tube tsohon Sarkin.