Wata kotun majistare da ke Ikeja, a Jihar Legas ta ba da umarnin a ci gaba da tsare wani mutum a gidan gyaran hali na Kirikiri bisa zargin sa da lalata wata yarinya ’yar shekara 14.
Mai gabatar da kara, DSP Kehinde Ajayi, ya shaida wa kotun cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne a 2022 a yankin Abaranje, Ikotun, Legas.
Ya ce wanda ake zargin ya lalata yarinyar; laifin da ya ce ya saba wa dokokin aikata laifuka na Jihar Legas (2015).
Alkalin kotun majistaren, Ejiro Kubeinje ya ba da umarnin mika takardun karar zuwa ga daraktan kararrakin jama’a don neman shawara.
Ya kuma dage shari’ar zuwa ranar 6 ga watan Fabrairu, 2024.
Laifin yana da hukuncin daurin rai-da-rai kamar yadda dokokin Jihar Legas suka tanada.