✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsinto gawarwakin iyalan Sarkin Mutumbiyu da aka sace a Jalingo

Lamarin ya tayar da hankalin al’ummar Masarautar Mutumbiyu.

An tsinci gawarwakin mutum bakwai na iyalan Sarkin Mutumbiyu da aka sace a Jihar Taraba.

Sarkin ya shaida wa wakilin Aminiya ta wayar tarho cewa an gano gawarwakin iyalansa wadanda wasu ’yan bindiga suka sace makonni biyu da suka gabata.

Sarkin mai daraja ta biyu, Alhaji Sani Muhammed ya bayyana cewa da safiyar ranar Asabar aka gano gawarwakin iyalan nasa su bakwai da suka hada da matansa biyu da ’ya’yansa biyar.

Ya ce an gano gawarwakin iyalansa ne a wani daji kusa da wani dutse a Karamar Hukumar Ardo Kola da ke jihar ta Taraba.

Bayanai sun ce an yi jana’izar mamatan a yau Asabar a garin Mutumbiyu.

Wannan lamari ya tayar da hankalin al’ummar Masarautar Mutumbiyu, inda kowa jikinsa ya yi sanyi kuma al’amura suka tsaya cik.

Aminiya ta ruwaito cewa makonni biyu da suka gabata ne wasu dauke da bindigogi wadanda ake tsammani masu satar mutane ne don neman kudin fansa suka sace iyalan basaraken a gidansa da ke garin Jalingo.

Sai kwanaki biyu da suka gabata ne daya daga cikin ’ya’yan nasa wani mai shekaru 14, ya kubuta daga hannun ’yan bindigar.