✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsinci gawar wata mata da danta a daki a Kano

Matar ta shafe kwana uku da rasuwa kafin makwabtanta sun gano.

An tsinci gawar wata mata mai suna Aisha Ishaq da danta mai wata shida a duniya a yankin ’Yan Awaki da ke Unguwa Uku a Karamar Hukumar Nassarawa a Jihar Kano.

An gano gawar matar ne bayan shafe kwana uku makwabtanta ba su ga motsinta ba.

Wani shugaban yankin mai suna Alhaji Ali Abdullahi Usman, ya ce matar wadda mijinta direban tanka ne, ta rasu a ranar Asabar amma ba a ankara ba sai da safiyar ranar Litinin.

Ya ce makwabtan matar ne suka ja hankalin ’yan unguwar bayan da suka fara jin wani wari na tashi daga gidanta.

Ya ce, “Da suka sanar da ni sai na je na fadawa ’yan sanda.

“Mun haura gidan da tsani, bayan mun karya kofar sai muka iske su a kwance cikin gidan sauro gawarsu ta fara rubewa.

“Dan nata shi ma ya rasu amma bai fara rubewa ba; da alama ta riga shi mutuwa.

“Ina zargin ya mutu ne saboda yunwa sakamakon uwar ta rasu ga shi ba abincin da zai ci.”

Ya ce ’yan sanda sun dauki gawar zuwa asibiti don gudanar da bincike.

Wani makwabcin matar mai suna Abubakar Muhammad, ya ce, “Matar ba ta da lafiya, amma mijinta bai dauka wata babbar cuta ba ce shi ya sa ya yi tafiyarsa.

“Kowa ya san tana rashin lafiya, amma babu wanda tunani ya zo masa don ya shiga gidan ya binciki me take ciki.”