An tsinci gawar wani dan sanda a yau da misalin karfe biyar na safe a kusa da kamfanin motoci na SCOA da ke Unguwar Shanu a jihar Kaduna.
Wakilin Aminiya ya gano cewa an harbi dan sandan ne sau uku a kirji da ciki da kuma kafada.
Wata majiya da ke yankin ta bayyana cewa dan sandan ya gamu da wasu ’yan fashi ne a kan hanyarsa ta dawowa gida daga aiki zuwa sabon bariki inda yake zaune.
Daya daga cikin mazauna yankin wanda bai so a bayyana sunansa ba ya ce “Mun samu gawar dan sandan lokacin da muka fito daga gidajenmu don yin sallar asuba, nan da take muka sanar da ’yan sanda. Da yawa sun yi zaton ya hadu da ’yan fashi ne yayin da suke dawowa daga fashi inda suka harbe shi suka yi awon-gaba da bindigarsa”. Inji shi.