✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsinci gawar Kanar din soja a Jos

An tsinci gawar Kanar BT Vandi (murabus) ne jim kadan bayan shigarsa daki a masaukin bakin

An tsinci gawar wani Kanar din sojan Najeriya mai ritaya a birnin Jos na Jihar Filato.

An ga gawar Kanar BT Vandi (murabus) ne a masaukin bakin sansanin sojoji na Defence Academy da ke kan titin Vom da ke Jos.

Ana zargin Kanar BT Vandi (murabus) ya rasu ne a yayin da yake tsaka da barci jim kadan da shigarsa daki a masaukin bakin.

Wani ma’aikacin masaukin bakin ne ya gano wagar Kanar Vandi (murabus) da misalin karfe 3.20 na ranar Laraba, sa’o’i kadan bayan dawowarsa.

A ranar Talata 16 ga watan uli 2023 Vandi ya fara sauka masaukin bakin, washegari kuma aka gano gawarsa.

An kai gawarsa Asibitin Rundunar Sojin Kasa ta Uku da ke Jos domin gudanar da bincike kan musabbakin rasuwarsa.

Wakilinmu ya nemi jin ta bakin Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar, Manjo Aliyu Danja, amma jami’in ya ce zai bincika labarin domin ya samu tabbaci a hukumance.