✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An tsige Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Imo

Majalisar ta yi wasu mambobinta shida kiranye da aka dakatar da su tun a watan Yuli.

Majalisar Dokokin Jihar Imo ta tsige Mataimakin Shugabanta, Amara Iwuanyanwu.

An tsige Iwuanyanwu yayin zaman majalisar na ranar Talata da aka tsaurara matakan tsaro bayan mambobinta 18 daga cikin 27 sun rattaba hannu kan amincewa da hakan.

Haka kuma Majalisar yayin zaman da Shugabanta, Paul Emezim ya jagoranta, ta yi wasu mambobinta shida kiranye da aka dakatar da su tun a ranar 8 ga watan Yulin bana.

Wannan kiranye dai na zuwa ne watanni hudu bayan Shugaban Majalisar ya dakatar da mambobin shida kan abin da ya kira sabawa dokokin majalisar.

’Yan majalisar da aka yi wa kiranye sun hada; Kennedy Ibe mai wakiltar Obowo, Onyemaechi Njoku mai wakiltar Ihitte Uboma, Uche Ogbuagu mai wakiltar Ikeduru, Anyadike Nwosu mai wakiltar Ezinihitte Mbaise, Philip Ejiogu, mai wakiltar Owerri ta Arewa, da Dominic Ezerioha mai wakiltar Oru ta Yamma.