✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Filato: An tsaurara matakan tsaro a Majalisa

An tsaurara matakan tsaro a harabar Majalisar Dokokin Jihar a safiyar Litinin.

Nn tsaurara makatan tsaro a Majalisar Dokokin Jihar Filato, inda aka jibge karin jami’an tsaro asafiyar Litinin.

Akawun Majalisar Dokokin Jihar Filato, Ponven Wuyen ya tabbatar wa wakinmu cewa an tsaurara matakan tsaro a majalisar da zagayenta, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

SAURARI: Yadda Labaran Kanzon Kurege Ke Haifar Da Illoli Ga Al’umma:

Sai dai ya ce sabanin wasu rahotanni da ke cewa jami’an tsaon sun rufe Majalisar, “Ba a rufe ta ba, domin yanzu haka ana gudanar da harkoki yadda aka saba, kuma yanzu haka ina cikin Majalisar.

“An kawo wasu jami’an tsaro, amma kuma ba wanda ke ce wa kowa komai.

“Jami’an tsaron Majalisar da aka sani suna nan a babbar kofar shiga kuma ma’aikata suna ta kai-komo ba tare da wata matsala ba.”

Idan za a iya tunawa, a yayin wani taron ’yan jarida da ta gudanar a ranar Asabar, Majalisar ta bukaci mutanen Jihar Filato su fito su kare kawunansu daga mahara da ke yin kisan gilla a sassan jihar.

Ta kuma ba wa Gwamnan Jihar, Simon Lalon wa’adin mako biyu ya magance matsalar tsaro da hare-hare a Jihar, sannan ya aiwatar da shawarwarin da ta ba shi, idan ba haka ba, ita za ta dauki matakin da take ganin ya dace.

Majalisar ta yi kiran ne bayan wasu mahara sun bi dare sun yi wa mutum kusan 30 kisan gilla a kauyen Yelwan Zangam da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa.

An kai harin na Yelwan Zangam ne kasa da mako biyu bayan an tare matafiya Fulani a yankin Gada-Biyu da ke Karamar Hukumar, aka kuma yi wa kusan mutum 30 daga cikinsu kisan gilla.

Sakamakon harin na biyu Gwamnatin Jihar Filato ta sanya dokar hana fita gaba da ya garin Jos, wanda a baya ta sassauta bayan kura ta soma lafawa bayan kisan gilla da aka yi wa Fulanin.