✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsaurara matakan tsaro a Abuja gabanin rantsar da Tinubu

Za a rufe manyan hanyoyin tsakiyar birnin tarayya saboda samar da tsaro yayin rantsar da Tinubu.

A karshen mako ne za a rufe hanyoyin tsakiyar Birnin Tarayya Abuja da su ka nufi hanyar dandalin Eagle Square, inda za a yi taron rantsar da sabuwar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Kama daga sojoji zuwa ’yan majalisar zartarwa sun yi tarukan bankwana da shugaba Muhammadu Buhari wanda zai bar Abuja zuwa Daura kai-tsaye daga  Eagle Square, wanda haka ne al’adar tun shekarar 2007 da tsohon shugaban kasa Obasanjo ya tafi Abeokuta a Jihar Ogun.

Jonathan ya tafi mahaifarsa Otuoke a Jihar Bayelsa a 2015 bayan mika mulki ga Buhari.

Tuni dai aka yi addu’o’i a Masallacin Abuja, a ranar Lahadi kuma za a yi addu’ar neman zaman lafiya a Babbar Majami’ar Tarayya.

A yayin jawabin bankwana, shugaba Buhari ya bukaci wadanda ba su ji dadin matakan da gwamnatinsa ta dauka ba su yafe masa.

Kazalika, ya ja hankalin zababben shugaban kasa da mataimakinsa da su daura damarar tunkarar aikin da ke gabansu.

Shi ma a nasa bangaren, shugaba mai jiran gado, Tinubu ya ce ya san girman aikin da ke jiran sa, inda ya jadadda cewar ba zai bai wa ’yan Najeriya kunya ba.