Hukumomin kasar Libya sun sanar da gano gawarwaki 42 a wani katon kabari da aka binne mutane da dama a birnin Sirte, daya daga cikin yankunan da mayakan IS suka rike.
Hukumar Kula da Mutanen da Suka Bata a Libya, ta ce ma’aikanta sun zakulo gawarwaki 42 bayan samun bayanai akan kabarin.
- An cafke Likitan da aka tono gawarwakin mata a ofishinsa
- Canjin Rayuwa: Mun yi amfani da yajin aikin ASUU —Daliban jami’a
Sanarwar ta ce tuni aka dauki kwayoyin hallita daga cikin gawarwakin domin gudanar da binciken likita akai.
Mayakan IS sun karbe iko da Birnin Sirte tsakanin shekarar 2015 zuwa 2016 sakamakon tabarbarewar tsaro a kasar, tun bayan kifar da gwamnatin shugaba Moammar Ghadafi a shekarar 2011.
Kungiyar da ke yaki da azabtar da mutane a duniya ta ce mutane sama da 500 kungiyoyin ’yan bindiga suka kashe a Libya daga watan Oktobar bara zuwa Agustan da ta gabata.
Duk da kokarin sasanta rikicin kasar Libya, har yanzu yan bindiga na ci gaba da iko da sassan kasar.