Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta ce akalla mutum hudu ne suka mutu, wasu shida kuma aka ceto su daga ginin bene mai hawa 21 da ya rushe a Jihar Legas.
Rahotanni sun ce benen, ya rufta ne lokacin da ake tsaka da aikin gina shi a unguwar Ikoyi a birnin Legas, da misalin karfe 1:00 na ranar Litinin.
- Da yawan ’yan APC ba su iya mulki ba – Dalung
- ’Yan sanda sun kama masu sarrafa gurbatacciyar giya a Fatakwal
Jami’in Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) shiyyar Kudu maso Yamma, Mista Ibrahim Farinloye, ne ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) hakan a Legas.
Makwabtan wurin da lamarin ya faru kuma sun ce kimanin mutum 50 zuwa 60 ne ake kyautata zaton ginin ya danne.
Galibin mutanen dai ma’aikata da magina da kuma injiniyoyin da ke aiki a gidan ne ifitila’in ya ritsa da su.
Tuni dai jami’an hukumar ta NEMA da kuma takwararta ta Jihar Legas, LASEMA, suka dukufa ci gaba da kokarin zakulo mutanen da ginin ya danne. (NAN)