Wasu manyan hafsoshi a Hedikwatar Rundunar ’Yan Sanda Najeriya da na Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi za su shiga hannu kan badakalar fataucin hodar Iblis.
Majiyoyi masu tushe sun tabbatar da haka ne bayan NDLEA ta cafke DCP Abba Kyari — wanda aka dakatar kan Badakalar Hushpuppi — kan zargin hannunsa a sabuwar badakalar.
- DCP Abba Kyari: Tashe da faduwar fitaccen dan sanda mai yaki da manyan laifuka
- ’Yan sanda sun cafke Abba Kyari sa’o’i bayan NDLEA ta ba da shelarsa
Kawo yanzu Abba Kyari ya shafe kwana guda a tsare a hannun hukumar NDLEA tana masa tambayoyi tare da wasu wadanda ake zargi domin gano irin rawar da kowannensu ya taka a cuwa-cuwar.
A ranar Litinin NDLEA ta sanar da neman Abba Kyari ruwa a jallo kan zargin sayar da hodar Iblis ta hannun Rundunar ’Yan Sanda (IRT) a karkashin jagorancinsa a filin jirgi na Enugu a watan Janairu.
Zargin cinikin hodar Iblis din ya tayar da kura ganin cewa tun a shekarar 2021 Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta dakatar da shi daga aiki tana bincike a kanshi bisa zargin aikata wasu manyan laifuka.
Majiyarmu ta ce, “Ba komai ke kawo wa binciken da ake wa Kyari a yanzu da sauran na baya tafiyar hawainiya ba face wasu manya da sauran wadanda aka ambaci sunansu.
“Akwai wasu manyan hafsoshi da suke da hannu a ciki kai-tsaye kuma suna sane cewa za a gano su, shi ya sa suke ta kawo wa batun tafiyar hawainiya,” a cewar majiyar.
Kama shi ta tayar da kura
A ranar Litinin ne dai batun karkatar da hodar Iblis mai nauyin kilogarm 25 da ake zargin DCP Abba Kyari da yi ya fito fili.
Ba a jima ba a ranar Hedikwatar ’Yan Sandan Najeriya ta kama shi, ta mika wa hukumar, lamarin da labarinsa ya karade Najeriya.
Rundani a tsakanin ’yan sanda
Bayan kama shi, an yi ta tattaunawa da muhawara a kan lamarin a tsakanin kananan jami’a da manya a hedikwatar rundunar.
Masu goyon bayansa dai sun kasance cike da mamaki tare da nuna shakku kan abin da ke faruwa, amma masu tababa a kan yanayin rayuwarsa sun ce da ma sun san akwai ranar kin dillanci.
Daya daga cikin hafsoshin da suka kama Abba Kyari suka mika shi ga NDLEA ya shaida wa wakilinmu cewa abun ya haifar da rudani da tsakanin ’yan sanda.
“Wannan abin ya taba mutuncin Hukumar ’Yan Sanda ne gaba daya; ’Yan sanda da yawa, musamman kananan ’yan sanda irinmu muna kallon Oga Kyari a matsayin abin koyi saboda irin nasarorin da ya samu wajen maka masu manyan laifi a fadin kasar nan.
“Ga shi kuma wannan zargi na miyagun kwayoyin na zuwa ne a daidai lokacin da muke jira mu ga yadda Badakalar Hushpuppi za ta kare,” inji dan sandan da wakilinmu ya zanta da shi ranar Litinin da dare.
Ba yanzu farau ba
Shi kuma wani dan sanda cewa ya yi ba bakon abu ba ne irin wannan hadin bakin da ke yi tsakanin Kyari da jami’an hukumar NDLEA.
“Wannan ba wani sabon abu ba ne. Ana sayar da kayan da aka kwace, har da tabar wiwi, mutane ne kawai ke mamaki.
“Tabbas akwai bara-gurci a cikin ’yan sanda da hukumar NDLEA da sauran hukumomin tsaro, musamman a filayen jirgin sama,” inji shi.
An kama mutum 5 tare da Kyari —NDLEA
Tun ranar Litinin, kakakin hukumar NDLEA na kasa, Femi Babafemi, ya sanar cewa hukumar ta kama wasu mutum biyar tare da Abba Kyari, saboda zargin.
Mutanen sun hada da ACP Sunday J. Ubua, ASP Bawa James, Infekta Simon Agirgba da Infekta John Nuhu.
Dukkansu an kawo su Hedikwatar NDLEA ne da misalin karfe 5 na yamma, aka kuma mika su a hukumance domin su amsa tambayoyi.
Babafemi ya ce, “Za a yi cikakken bincike domin tabbatar da ganin wadanda suka shiga hannu da sauran da suka rage sun girbi abin da suka shuka.”
Tun da farko, Babafemi ya shaida wa taron manema labarai cewa wani bincike da suka gudanar ya nuna Abba Kyari memba ne na masu safarar miyagun kwayoyi na kasa da kasa.
Ya ce hukumar ta shelanta cigiyar sa ruwa a jallo ne saboda duk kokarin da ta yi na ganin ya amsa gayyatar da ta yi masa ya ci tura.
“Bayanan da muka samu sun nuna DCP Abba Kyari memba ne a kungiyar masu fataucin miyagun kwayoyi a tsakanin Brazil da kasar Habasha da Najeriya, kuma yana bukatar amsa tambayoyi kan kes din kyayoyin da muke bincike, wanda kuma shi ne babban wanda ake zargi.
“Rashin zuwansa shi ya sa ba mu da zabi face mu yi abin da muka yi,” inji Babafemi.