✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tarwatsa masu zanga-zanga da barkonon tsohuwa a Gonin Gora

Zanga-zangar ta zame wa matafiya kadagaren bakin tulu a babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Jami’an tsaro sun tarwatsa wasu matasan unguwar Gonin Gora da ke Karamar Hukumar Chikun da suka tare babban titin Kaduna zuwa Abuja da sunan zanga-zanga.

Matasan sun fito ne domin nuna fushinsu kan zargin kashe wasu mutum biyu tare da sace wasu fiye da goma da ’yan fashin daji suka yi.

Bayanai sun ce ’yan fashin dajin sun yi wa Unguwar Auta da ke Gonin Gora dirar mikiya ne a daren jiya Laraba, inda suka halaka ’yan sintiri biyu tare da sace mutane sama da goma a unguwar.

Wannan lamari ne ya fusata mata da matasan unguwar har suka fito kan titin Kaduna zuwa Abuja suna zanga-zangar adawa da lamarin.

Aminiya ta ruwaito cewa, zanga-zangar ce ta zame wa matafiya kadagaren bakin tulu, inda suka shafe tsawon sa’o’i suna zaman dabaro har zuwa lokacin da jami’an tsaro suka tarwatsa masu zanga-zangar da barkonon tsohuwa.

Wani dan unguwar mai suna Yusuf Sarki, yayin zantawa da Aminiya ya tabbatar da kisan mutum biyun da ya ce ’yan bindigar sun harbe da bindiga.

“Mutum biyu ne aka kashe sannan kuma aka sace mutane a gidaje kusan goma da ’yan fashin dajin suka shiga cikin daren,” inji shi.

Kazalika, Aminiya ta ruwaito cewa ’yan fashin dajin sun kuma kona wata motar sojoji a yankin Ligari yayin da suka yi yunkurin yi musu tara-tara a ƙoƙarin ficewa daga unguwar.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya jagoranci shugabannin jami’an tsaro zuwa unguwar domin bai wa matasan Gonin Gora hakurin domin buɗe wa matafiya hanya su samu damar wucewa.

Ya kuma bayyana rashin jin daɗinsa kan yadda mutanen unguwar suka tare titin, yana mai cewa ba su da hujja a kan hakan domin kuwa jami’an tsaro na ƙoƙarin magance matsalar tsaro a jihar.

Ya kuma bayyana cewa jami’an tsaron da suka isa unguwar a cikin daren sun yi ba-ta-kashi da ’yan fashin dajin wanda a dalilin haka suka samu nasarar kubutar da wasu daga cikin waɗanda aka sace daga gidajensu.

Kazalika, Mista Aruwan ya ce jami’an tsaro na ci gaba da bibiyar sahun waɗannan ’yan fashin daji domin su girbi abin da suka shuka.