A nasa ɓangaren, Shugaban Rukunin Kamfanonin BUA, ya ba da gudunmawar Naira biliyan biyar.

Tsohon Ministan Taro kuma Shugaban Gidauniyar TY, Janar Theophelus Ɗanjuma, ya bayar da Naira biliyan uku.

Babban attajiri a yankin Kudu, Arthur Eze, ya ba da Naira miliyan 500.

Sanata Sani Musa ya ba da miliyan N250 a yayin da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ba da miliyan N50.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Barau Jibrin ya ba da Naira miliyan 20 a yayin da Sanata Aliyu Wadada ya ba da miliyan 10.

Hamshakiyar ’yan kasuwa Folorunsho Alakija, da wasu fitattun ’yan Najeriya sun bayyana gudunmawa, amma ba su sanarna bainar jama’a ba.

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci tsoffin shugaban kasa na farar hula na mulkin soji irinsu Goodluck Jonathan, Yakubu Gowon, Abdulsalami Abubakar, da wasu manyan baƙi.

Tsoffin mataimakan shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar da Muhammad Namadi Sambo da Yemi Osinbajo.

Hakazalika dan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar NNPP Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da takwaransa na Jam’iyyar LP, Peter Obi, sun samu halartar.