✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An taba hana ni shiga gida a Fadar Shugaban Kasa – A’isha Buhari

Uwagidan  Shugaban  Kasa Muhammadu Buhari Hajiya A’isha Buhari ta yi karin haske dangane da wata tirka-tirkar da ta faru tsakaninta da iyalin Mamman Daura, a…

Uwagidan  Shugaban  Kasa Muhammadu Buhari Hajiya A’isha Buhari ta yi karin haske dangane da wata tirka-tirkar da ta faru tsakaninta da iyalin Mamman Daura, a cikin Fadar Shugaban Kasa a Abuja.

A cikin wata tattaunawa da gidan Radiyon BBC, A’isha Buhari ta tabbatar da cewa ita ce a cikin bidiyon da aka nuno tana hargowa saboda kulle m ta kofar shiga gidan da aka yi.

Sannan A’isha Buhari ta ce ’yar Alhaji Mamman Daura ce mai suna Fatima ta kulle kofar, kuma ita ce ta rika daukarta da bidiyon wayarta a gaban jami’an tsaronta.

“Na je domin in ga yanayin dakunan gidan, amma sai iyalin Mamman Daura suka hana ni shiga gidan, saboda sun kulle kofar. Daga nan sai na kewaya ta wata kofa a baya. Nan ma na same ta a kulle,” inji A’isha Buhari.

Ta yin karin haske da cewa: “Jami’an tsarona suna wurin amma sun kasa yin komai domin ’yar gidan Mamman Daura – Fatima ce ta dauki bidiyon kuma har yau ni da su mun kasa yin komai kan lamarin.”

Haka zalika a hirar da aka yi a harshen Hausa ta nanata cewa Fatima ce ta dauki bidiyon, har tana yi mata dariya kuma ita ce ta rufe mata kofar dakin ajiyar kayayyaki.

A hirarta da BBC, Fatima ta bayyana cewa tun bayan hawan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari mulki, shugaban ya bai wa mahaifinta (Mamman Daura) wurin zama a cikin fadar Shugaban Kasa.

Ta bayyana cewa ko da A’isha Buhari ta zo ta ga kofar a rufe, ta yi amfani da kujerar karfe wajen balle kofar.”