An soma jigilar maniyyatan Hajjin bana 3,888 daga Jihar Sakkwato a ranar Talata.
Aminiya ta ruwaito cewa jirgin farko ya tashi da maniyata 432 da suka hada da maza 242 da mata 180 da ma’aikata bakwai.
Gwamna Ahmad Aliyu da Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar da Ministan Sufuri Festus Kiyamo sun halarci ƙaddamar da tashin jirgin na farko da maniyyatan na Sakkwato.
Gwamnan Ahmad Aliyu ya ba da sanarwar bayar da kyautar riyal dubu ɗai-ɗai da naira dubu 500 kuɗin Najeriya ga dukkan maniyatan.
Gwamnan ya bukaci maniyyatan da su zama jakadu nagari da za su riƙe mutuncin jiha da ƙasa baki ɗaya.