Rundunar ’yan sandan Jihar Enugu, ta kaddamar da bincike kan abin da ya yi sanadin mutuwar wasu mutane biyar ’yan gida daya.
Wata sanarwa da jami’in yada labaran rundunar DSP Daniel Nduke ya fitar ta ce, lamarin ya faru ne a ranar Asabar da misalin karfe 9:25 na safe a unguwar Obollo-Afor da ke Karamar Hukumar Udena ta jihar.
- Hadarin mota ya yi ajalin mutum 3 a Neja
- Gwamnati za ta rage kashi 30 na cunkuso a gidajen gyaran hali
Sanarwar ta ce, “Kwamishinan ’yan sandan Jihar Enugu, CP Ahmed Ammani, ya ba da umarnin a gudanar da cikakken bincike don gano abin da ya yi sanadin mutuwar farar-daya da ta samu Chinyere Odoh.”
Chinyere ta rasu ne tare da ‘ya’yanta biyu – Udochukwu Odoh mai shekaru bakwai da Chukwuemeka Odoh mai shekaru 4.
Haka kuma akwai kanenta mata biyu – Martina Ezeme da Ngozi Ezeme kamar yadda sanarwar ta DSP Nduke wacce aka wallafa a shafin Facebook din rundunar ta nuna.
Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa, mutanen sun kwanta lafiya, amma da aka wayi gari da safe sai ba a ji duriyarsu ba, da aka duba sai aka tsinci gawarwakinsu a dakunansu.
“Sai da aka fasa kofofin dakunan da suka kwana a ciki,” in ji Nduke.
Kwamishina Ammani ya kwatanta lamarin a matsayin abin takaici yana mai mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalai da abokan mamatan.