✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An shigo da madarar Naira biliyan 27 Najeriya cikin wata 3

Hakan na faruwa ne duk da yunkurin gwamnati na dakile shigo da kaya

Duk da yunkurin Gwamnatin Tarayya na tabbatar da dogaro da kai wajen samar da madara a kasar nan tare da dakile hanyoyin samun kudin musaya don shigo da madara, bayanai sun ce an shigo da madarar da ta kai ta Naira biliyan 27 da miliyan 664 a cikin wata uku na farkon wannan shekarar.

Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ce ta bayyana haka a wani rahoto da ta fitar, inda ta ce, an shigo da madarar ce daga kasashe hudu.

’Yan kasuwar da suka shigo da madarar sun yi bad-dasawu wajen nuna sun shigo da kayayyakin yin madarar ne daga kasashen Ireland, wadda ta kai ta Naira biliyan 16.1, sai Malesiya Naira biliyan 5.5 sai Jamus Naira biliyan 4.8 sai kuma Faransa Naira biliyan 1.

An kashe wadannan kudi ne a daidai lokacin da Gwamnatin Tarayya ke shirin haramta shigo da madara cikin kasar nan.

Gwamnatin tana son haramta shigo da madarar ce saboda kayayyakin samar da madarar da ta ce ta samar, inda a shekarar 2020 tsohon Ministan Gona, Alhaji Sabo Nanono ya ce Gwamnatin Tarayya ta shirya don hana shigo da madara zuwa kasar nan a shekara 2022.

Ya ce akwai shanu sama da miliyan 25 a kasar nan da za a iya amfani da su wajen samar da madara lita miliyan biyar a kowace rana.

Kudin da aka kashe wajen shigo da madarar ya gaza wanda aka kashe wajen shigo da ita a bara da Naira biliyan 4.

Amma raguwar ba ta kai yadda Gwamnatin Tarayya take so ba a kokarinta na hana shigo da madara daga kasashen waje.