✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An shawarci jama’a su sassauta burinsu ga gwamnati

A karshen watan jiya ne kungiyar sashen kimiyyar siyasa ta gudanar da taronta na shekara-shekara a Jami’ar Jihar Nasarwa da ke garin Keffi. Farfesa Shu’aibu…

A karshen watan jiya ne kungiyar sashen kimiyyar siyasa ta gudanar da taronta na shekara-shekara a Jami’ar Jihar Nasarwa da ke garin Keffi.

Farfesa Shu’aibu Ibrahim wanda shi ne shugaban kwamitin tsare-tsaren kungiyar, ya shawarci ’yan Najeriya da su kasance masu sassauta burinsu ga gwamnati kasar nan, “domin sai a hakalin ne za a ga canji, ba da garaje ba.”
Farfesa Shu aibu ya kara da cewa: “Mulki ba abu ne na sha yanzu magani yanzu ba.” Daga bisani ya jinjina wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari game da irin salon mulkin da ya dauka.
Akawun Majalisar Tarayya Alhaji Salisu Mai Kusuwa a jawabinsa ya ce “nayi matukar farin ciki. Na mika sakon fatan alheri a wannan taron kungiyar kimiyyar siyasa na kasa na bana.
Kuma zan so in nuna farin cikina zuwa ga shugabanni da kuma mambobin kungiyar, domin kasancewarta mai fafutukar ganin Najeriya ta ginu da tubali mai inganci, kana zan so duk dan kasar nan yakasance mai dogaro da kansa ba mai dogaro da gwamnati ba, domin hakan shi ne kadai hanyar da zamu san ’yancin kanmu da kuma gyara tattalin arzikin kasarmu,”inji shi.