Na’ibin limamin babban masallacin juma’a na Abuja Dokta Ibrahim Makari ya bukaci iyaye musamman ma mata su rika sanya idanu a kan karatun ‘ya’yansu don a samu ilimi mai inganci.
Ya yi wannan kiran ne a lokacin da Malami a tsangayar koyar da karatun lauya na Jami’ar Ahmadu Bello Zariya Dokta Ibrahim Jibrin Sulaiman ya wakilce shi yayin bikin yaye dalibai karo na tara da makarantar Nurul Bayan International Academy da ke Abuja ta yi a ranar Asabar da ta gabata
Ya ce: “Babu wanda zai yi nasara sai yana da ilimi, ko yanzu ma ana yaki da alkalami ne, idan babu ilimi ba za a yi hakan ba. Don haka ya kamata iyaye musamman ma mata su rika sanya idanu a kan karatun ‘ya’yansu don a samu ilimi mai inganci. Na karfafa a kan iyaye mata ne saboda sun fi kusaci da yara, kasancewar mahaifinsu kullum na wurin neman abinci.”
Ya nemi yara su zage damtse wurin mayar da hankali a kan karatu, domin ta haka ne za su kai ga cim ma nasara, inda ya ba da misalin a duba makera da kuma masu maganin gargajiya, a dalilin rashin karatu mai zurfi ne ya sanya likitocin zamani da kuma kamfanin kere-kere suka zarce su.
Shugaban kungiyar Malamai da Iyaye (PTA) Dokta Yusuf Abdullahi ya nemi iyaye su ci gaba da ba da hadin kai don a samu ilimi mai inganci.
Ya ce: “Idan iyaye suka ba da dukkan hadin kan da ake bukata, to ‘ya’yanmu za su samu ilimi mai nagarta. Kuma za mu rika alfahari da su.”
Shugaban makarantar Malam Taofik Adunfe Atitola a lokacin da yake jawabin godiya ga wadanda suka halarci taron, ya nemi sauran iyaye su kawo ‘ya’yansu don su samu tarbiyya da kuma ilimi mai nagarta.
Ya ce: “Zan yi amfani da wannan damar domin na yi kira ga sauran iyaye su kawo ‘ya’yansu wannan makaranta don su samu tarbiyya ta kwarai da kuma ilimi mai nagarta, saboda makarantar ta kunshi karatun boko da kuma na addini, kuma kowa ya san karatun boko babu na addini kamar matafiyi a cikin daji ne babu taswira.”
daliban da aka yaye sun hada da ‘yan ajin share fage da firamare da karamar sakandare da kuma babbar sakandare.
An shawarci iyaye mata su rika sa idanu a kan karatun ‘ya’yansu
Na’ibin limamin babban masallacin juma’a na Abuja Dokta Ibrahim Makari ya bukaci iyaye musamman ma mata su rika sanya idanu a kan karatun ‘ya’yansu don…