✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sasanta Ali Nuhu da Adam Zango bayan ’yar hatsaniya

A jiya ne aka sasanta fitattun jaruman fina-finan Hausa, Ali Nuhu da kuma Adam A. Zango bayan wata hatsaniya da ta barke tsakanin jaruman. Shahararren…

A jiya ne aka sasanta fitattun jaruman fina-finan Hausa, Ali Nuhu da kuma Adam A. Zango bayan wata hatsaniya da ta barke tsakanin jaruman.

Shahararren darakta Falalu Dorayi da kuma furodusa Sani Sule ne suka jagoranci batun sasantarwa a daren jiya, inda a karshe kwalliya ta biya kudin sabulu.

Jaruman sun sasanta, sun rungumi juna, sun yafe wa juna, inda suka dauki hotuna daban-daban, a cikin akwai wanda suke dariya a zuwan an mayar da komai ba komai ba.

A dangane da tushen abin da ya haifar da rashin jituwar tsakanin jaruman, sai wata majiya ta bayyana wa Aminiya cewa, wutar rikicin ta fara ruruwa ne a bara a lokacin da jarumi Ali Nuhu ya nuna fim dinsa mai suna ‘Mansoor’ a wata sinima da ke Shoprite a birnin Kano, inda Zango bai je ya kalli fim din, wannan ya sanya yaran Ali Nuhu suka fara guna-guni.

Majiyar ta ce: “Batun hatsaniyar ta kara habaka ne bayan Ali Nuhu ya ki zuwa kallon fim din ‘Gwaska Returns’ na jarumi Zango, wanda aka nuna a sinima a Kano a kwanakin baya, inda a nan ne yaran Zango suka ci gaba da guna-guni.

Majiya ta kara bayyana cewa amma batun hatsaniyar ta dauki sabon salo ne a lokacin da ake daukar fim din darakta Kamal S. Alkali a kwanakin baya, inda Zango ya zo wurin daukar fim din, sai aka samu Ali Nuhu ba shi da lafiya, inda yake kwance a wani daki.

“Bayan an sanar da Zango cewa Ali Nuhu na kwance ba shi da lafiya ne, sai ya ce ba zai je ya gaishe shi ba, al’amarin da ya sanya magoya bayan jaruman suka fara yakin cacar-baki a shafin Instagram,” inji majiyar.

Al’amarin da ana cikin haka sai Adam A Zango ya sanya hotonsa hade da wadansu kalamai da yaran Ali Nuhu suka zargi cewa da ubangidansu yake.

A cikin sanarwar Zango ya ce, “A yau wasu daga cikin jarumai MAZA da MATA, tsofaffi da manya da kananan da wani bangare na ma’aikata a Kannywood, suka kai kara da kukan wasu manyan furodusoshi da kananansu wurin Hukumar tace fina-finai, kan abin da suke kira danne hakki da mugunta da furodusoshin suke musu.”

Ya ce, a cewarsu mafi yawan ayyukan da suke yi, to furodusoshi din ba sa biyansu, ko kuma in za a biya ka, a ba ka kudin da ko na mota ba zai kai ba. Ko a yi kwanaki ana aiki da kai, in an gama a ce za a kira ka, shi ke nan an cinye.

“Tabbas duk abin da mutum sama da ashirin mata da maza suka fada, to lallai yana faruwa. Kuma hakan zalinci ne. Allah ba Zai kyale ba. Ya ku masu wannan dabi’ar, ku sani an wuce lokacin bauta. Wadanda kuke bautarwa Allah sai Ya saka musu.”

Hakan ya sa yaran Ali Nuhu suka taso kamar za su hadiye Zango, inda al’amarin da ya sanya Zango ya sake fitar da wata sanarwar cewa shi fa ba da Ali Nuhu yake rigima ba, yana yi ne da wasu gurbatattu a Kannywood wadanda ba su yarda da Allah ba.

Kamar rigimar ta kwanta sai kawai aka ga jarumi Bello Muhammad Bello (BMB) ya fito yana yi wa jarumi Ali Nuhu gorin asali.

Al’amarin da ya sanya komai ya kara rincabewa har aka kira BMB a matsayin mara asali, dalilin da ya sa fitaccen marubuci Yakubu M. Kumo ya fito da nasiha mai zafi ke nan.

Yakubu Kumo ya ce, bai taba magana a kan duk wani al’amari da ya shafi fadan ’yan fim ba, sai dai dole ya shiga duk wani al’amari da ya ci karo da shi, wanda ya ke ganin yana bukatar tsokaci a kan addini, duk da dai shi ba malami ba ne.

“Na ga wani rubutu da Bello M. Bello ya yi wanda shi a tunaninsa kamar vaba sunan Ali Nuhu yake son yi, ko kuma martani ne mai zafi ga masoyansa. Sai dai ni a gani na wannan rubutun kamar izgilanci ne ga addini, ko kuma shisshigi a kan kaddara da nufin Mahaliccinmu.

“Ya kamata Bello ya sani, Ali Nuhu dai Musulmi ne, duk abin da ya haife shi ba zai shafi Musuluncinsa ba, da shi da kai duk daya ne a wajen Allah. Bambancin kawai shi ne …Inna akramakum indallahi atkakum… (mafi soyuwa a wajen Allah shi ne wanda ya fi jin tsoronsa)…(Qur’an 49:13).

Ya ce, sannan idan ma mahaifinsa ba Musulmi ba ne, to BMB ba shi da tabbacin a haka zai mutu, tun da hadisi ya karantar da cewa, wasu sai a karshen lokacinsu suke samun sa’ar shiga aljanna, ke nan ashe babu wanda ya san makomar wani sai Mahaliccinmu.

“Don haka ba wani abin fada ba ne don mutum ya kasance Musulmi, sannan uba ba Musulmi ba, in har za ka zagi Ali Nuhu saboda wannan sai ka koma ka hada da Annabi Ibrahim, saboda shi mahaifinsa ba ma Kirista ba ne, Kafiri ne mai bautar gumaka (Ka karanta Suratul Maryam)

“Don haka in har Annabi Ibrahim (AS) wanda a tsatsonsa Annabawa kamarsu Annabi Musa, Annabi Isma’il, Annabi Isa da Mafificin halitta Annabinmu Muhammad (SAW) suka fito, to waye kuma Ali Nuhu. Saboda irin wannan tunanin ne Allah Ya sake kafa misali a Suratul Tahrim, inda aka nuna matar Annabi Lut ma ba Musulma ba ce, haka kuma dan Annabi Nuhu. Sannan Allah Ya nufi matar Fir’auna da yin imani duk da kafircewarsa.

Ya kara da cewa kowa da yadda Allah Ya nufa zai zo duniya, kuma babu wanda ya isa ya kauce wa hakan, babu wanda Allah Ya shawarta a lokacin da za a halicce shi, kowa tsintar kansa ya yi a duniyar.

Wannan batu na marubuci Kumo ne ya sanya dan ganin kasha-nin Zango, wanda a rikicin baya saboda kare Zango har ’yan sanda ne suka kama shi, wato Ali Artwork, inda ya bayyana cewa duk abin da aka ga Ali da Zango suna yi, to suna sane, kuma su suke kirkirar hakan don su motsa jam’iyya, kada a ce an kwana biyu an manta da su.

Ya ce, “To ku sani ku masoyansu ku suka mayar ba ku san me kuke yi ba, domin in ba ku manta ba a shekarun baya sun taba shirya irin wannan rikicin nasu, muka zo mu kai ta cece-kuce a kai, amma daga qarshe mai hakan ta haifar? Sai suka mayar da mu ba mu san komai ba.

Ana cikin hakan ne sai Ali Nuhu ya fitar da sanarwar cewa yana rokon masoyansa su daina batanci ga kowa.

Ya ce, “Ina rokon duk masoyana maza da mata, duk wanda ya san tsakani da Allah yake so na, ya daina rubutu don cin mutunci ga wani ko wata. Ba na rigima ko batanci ga duk wani abokin sana’ata, sannan duk wanda ya yi mini ku bar shi da Allah. Babu sakayyar da ta wuce ta Allah.”

Bayan an kai ga sasantarwar jiya ne sai a yau jarumin barkwanci Ali Artwork ya sake dawowa inda ya ce, “Yanzu kun gamsu da rubutuna, ga shi har sun shirya, sun gama shirya muku fim din kun hau kun zauna, ku kuma masu kunfar baki taku ta kare.”

A yanzu dai an kai ga sasanta wadannan jarumai, abin jira a gani shi ne ko sasantawar za ta dore.