Mahukunta a Kasar Somaliya sun yanke shawarar gudanar da zaben sabon shugaban kasa bayan wani zaman tattaunawa na kwanaki biyu da suka gudanar a Mogadishu, babban birnin Kasar.
A yunkurinsu na kawo karshen takaddamar siyasar kasar, masu ruwa da tsakin sun ce za su zabi sabon shugaban ne daga cikin ’yan Majalisar Tarayyar kasar kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito.
Firaiministan Somaliya, Mohamed Roble, ya ce sun yanke shawarar gudanar da babban zaben kasar a ranar 10 ga watan Oktoban bana.
A cewarsa, wannan mataki na zuwa ne biyo bayan wata doguwar tattaunawa tsakanin Kwamitin Dattawan Kasa da jam’iyya mai mulki.
Kazalika, ya ce za a gudanar da zaben ’yan shugabannin Majalisar Dattawa a ranar 25 ga watan Yuli, yayin da kuma za a gudanar da na sauran ’yan majalisar daga 10 ga watan Agusta zuwa 10 ga watan Satumba.
Bayanai sun ce ana ci gaba da samun takaddama kan siyasar kasar tun bayan da wa’adin mulkin Shugaba Mohamed Farmajo na tsawon shekaru hudu ya kare a ranar 8 ga watan Fabrairu yayin da kuma na ’yan Majalisar Tarayyar ya kare tun a ranar 27 ga watan Dasumba.