An sanya na’ura da za ta rika bayar da fatawa cikin harshen Hausa da sauran harsuna a Masallacin Harami domin saukake wa masu ibada samun bayani nan take.
Butum-butumin da aka nadada a bangaren mata da wasu wurare a Masallaci Mai Alfarma da ke birnin Makkah, zai rika samar da amsoshi kai-tsaye ga masu tambaya game da ayyukan ibada a cikin harsuna 11 ciki har da harshen Hausa.
- Kungiya ta raba wa marasa galihu kayan abinci da tufafi a Ajingi
- Ranar 17 ga Ramadan aka yi Yakin Badar
Hukumar gudanarwar Masallatai Masu Alfarma ta ce na’urar za ta rika hada masu tambaya kai-tsaye da manyan mamalan Saudiyya domin yi musu bayani daga ko’ina.
Hakazalika na’urorin za su rika samar da muhimman bayanai ga masu ziyarar Umrah da aikin Hajji kan ayyukan ibada da suka dangance su, gami da kwatancen inda suke son zuwa a cikin masallacin.
Harsunan da na’urar take amfani da su sun hada da Larabci, Hausa, Turancin Ingilishi, Faransanci, Farisanci, Turkanci, Urdu, Chanisnaci, Bengali, Malay, da kuma Rashanci.
Butum-butumin, wanda ke tafiya da tayoyi, an kera shi ne da fasahar da yake iya tsayawa da kansa a wurin mai neman fatawa, shi kuma sai ya latsa, ya yi tambayarsa, nan take za a hada shi da malamin da zai amsa masa tambayarsa kai-tsaye, ta bidiyo.
Baya ga kyamarori da makirfon masu karfin gaske da wannan na’urar fatawa take dauke da su, tana amfani ne da fasahar sadarwa ta Wi-Fi mai karfin 5 GHz, domin tabbatar da karfin layin sadarwa tsakanin masu tambaya da malamai.