✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An sanya dokar hana fita a Legas

Gwamnatin Jihar Legas ta sanya dokar hana fita ta sa'a 24 a fadin jihar

Gwamnatin Jihar Legas ta sanya dokar hana fita ta sa’a 24 a daukacin jihar.

Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya sanya dokar bayan wata arangama da aka yi a zanga-zangar #EndSARS inda aka hallaka mutum uku da safiyar Talata.

“Saboda haka na ayyana dokar hana hana fita na sa’a 24 a duk fadin jihar daga karfe 4 na yammacin yau 20 ga Oktoba, 2020.

“Kada wanda ya sake aka kama shi a kan titi matukar shi ba ma’aikacin agaji ko ma’aikaci na musamman ba ne”, inji sanarwar da ya fitar.

Gwamna Sanwo-Olu ya ce gwamnatin jihar ba za ta zura ido wasu na fakewa da zanga-zangar ta #EndSARS suna kashe kashe da sare-sare ba.