✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dokar hana fita a Ekiti sai baba ta gani

Gwamnan Jihar Ekiti ya sanya dokar hana fita ta sa’a 24 har sai abin da Allah Ya yi a fadin jihar. An sanya dokar ce…

Gwamnan Jihar Ekiti ya sanya dokar hana fita ta sa’a 24 har sai abin da Allah Ya yi a fadin jihar.

An sanya dokar ce bayan ‘yan daba da wasu bata-gari sun kwace zanga-zangar #EndSARS a jihar, tare da tayar da hankulan jama’a.

Gwamnan ya ba da umarnin tsawaita dokar hana fitar ne a daidai lokacin da wadda ya sanya da farko ke dab da karewa.

Hakan na dauke ne a cikin sakon Sakataren Watsa Labaran gwamnan, Yinka Oyebode ya fitar.

Karin labarin na tafe…