Ma’aikatar Ilimin jihar Enugu ta sanar da ranar 18 ga watan Janairun 2021 a matsayin ranar da za a sake bude makarantu a jihar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ilimin jihar, Farfesa Uche Eze ya sanya wa hannu.
- An soke lasisin makarantu masu zaman kansu 500 a Zamfara
- COVID-19: An bayyana ranar sake bude makarantu a jihar Legas
- Sai ranar 18 ga Janairu za a bude manyan makarantu
Kwamishinan ya ce an amince da ranar ne sakamakon cimma matsaya da aka yi a taron masu ruwa da tsaki na jihar.
Farfesa Uche ya ja hankalin makarantun jihar da su tabbatar da bin matakan kariyar cutar Korona da zarar an bude makarantun.
Ya kara da cewa Ma’aikatar Ilimin jihar za ta yi bincike don gano makarantun da ba sa bin matakan kariyar.
Daga nan sai Kwamishinan ya bukaci makarantun jihar da su fito da dabarun koyawa yara karatu ta intanet, don rage cunkoso a cikinsu.