✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An samu nasarar yi wa Gareth Bale aiki

A shekaranjiya Laraba ne mahukunta kulob din Real Madrid na Sifen suka bayar da sanwar Likitoci sun samu nasara a aikin da suka yi wa…

A shekaranjiya Laraba ne mahukunta kulob din Real Madrid na Sifen suka bayar da sanwar Likitoci sun samu nasara a aikin da suka yi wa dan kwallon gabansu Gareth Bale.
Gare Bale wanda ya samu matsala a kokon kafarsa ta dama a wasan da kulob din ya yi da na Sporting Lisbon a gasar zakarun kulob-kulob na Turai a kwanakin baya, an yi masa aiki ne a wani asibiti da ake kira King Edward bII Hospital da ke birnin Landan.
Jim kadan bayan an kammala aikin ne sai kulob din ya bayar da sanarwa a shafin sadarwarsa na Twitter cewa “an samu nasara a aikin da aka yi wa Gareth Bale”.
Sai dai kulob din bai bayyana takamaiman lokacin da dan kwallon zai kwashe yana jinya ba, amma masana harkar kwallon sun yi hasashen zai shafe kimanin watanni uku yana jinya ba tare da ya buga kwallo ba.
Kenan, dan kwallon ba zai buga wasan gobe a tsakanin FC Barcelona da na Madrid ba da kuma wasan Real Madrid da Borussia Dortmund a ranar Laraba mai zuwa.
Ana sa ran Gareth Bale zai koma fagen dage ne a watan Maris na shekara mai zuwa.