Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Zamfara ta ce an samu gobara sau 767 a fadin Jihar a shekarar 2020.
Mukaddashin Daraktan Hukumar, Abdullahi Jibbo, ya ce ba a taba samun yawan gobara irin yadda aka samu 2020 a jihar ba cikin shekaru 10 da suka wuce.
Da yake bayani a Gusau a ranar Alhamis, Abdullahi Jibo, ya ce yawancin gobarar sun tashi ne sakamakon sakaci da kayan laturoni da kuma kin bin ka’idojin kare aukuwar gobara a gidaje da wuraren kasuwanci.
Ya ce Gusau ita ce Karamar Hukumar mafi yawan gobara a shekarar inda aka samu 237, Kaura Namoda 116; Talata Mafara 112; Tsafe 85 sai Gummi, 77.
Ya shawarci jama’a su guji yin abubuwan da ke iya haddasa tashin gobara, hukumomi kuma su tabbatar da bin matakan kare aukuwarta a dukkannin kasuwanni.
Abdullahi ya kuma gargadi mutane su guji ajiye kayan fetur a gidajensu, inda ya ce jami’an hukumar na zagawa a Jihar domin tabbatar da ana bin dokokin kare aukuwar gobara, musamman a wuraren kasuwanci.
Sauran kanan hukumomin Jihar Zamfara da aka samu gobarar a cewarsa su ne: Anka 56, Shinkafi 36, Bungudu 32, Maru 28, Bakura ma 28 sai kuma Nasarawa 13.
An samu 11 a Birnin Magaji, 10 a Maradun, Jangebe 10, Kasuwa Daji 10 , Zurmi 8, Dansadau 6 sai kuma Bukkuyum 4.