✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An samu gagarumar ci gaba a shekara 40 na Sarkin Lafiya – Madakin Lafiya

Alhaji Isyaka Dauda, sabon Madakin Lafiya tsohon ma’aikacin gwamnati ne da ya rike mukamai daban-daban da kuma sarautun gargajiya da dama kafin ya zama Madaki.…

Alhaji Isyaka Dauda, sabon Madakin Lafiya tsohon ma’aikacin gwamnati ne da ya rike mukamai daban-daban da kuma sarautun gargajiya da dama kafin ya zama Madaki. A hirarsa da wakilinmu ya bayyana nasarori da mai martaba Sarkin Lafiya Alhaji Isa Mustapha Agwai na daya ya samu a shekara 40 a gadon sarauta, kuma ya tabo batutuwan da suka shafi siyasa musamman yunkurin tsige Gwamna Umaru Al-Makura na Jihar Nasarawa da sauransu:

Ya lallabai a takaice wadanne mukamai ka rike kafin nada ka Madakin Lafiya?
A takaice bayan na kammala karatuna na yi aikin gwamnati na kuma taba siyasa. A karshe na dawo gida nan Lafiya fadar Jihar Nasarawa inda da yake na gaji sarauta sai Mai martaba Sarkin Lafiya Alhaji Isah Mustapha Agwai ya nada ni sarautar Magajin Gari, daga nan sai na samu sarautar Dallatun Lafiya inda daga bisani ya sake nada ni Magajin Garin Lafiya. Daga wannan sarauta ce na zama Madakin Lafiya a yanzu haka.
Yaya za ka bambanta yanayin aikinka a matsayin Madakin Lafiya da sarautun da ka rike a baya?
Da farko dai lokacin da nake Magajin Gari akwai wani yanki a nan Lafiya da ake kira Akunza inda na kasance Hakimin yankin. Na yi aiki ne a karkashin karamar Hukumar Lafiya. A lokacin ina sasanta rigirgimu a tsakanin al’ummar yankina ne kawai wato Akunza. Amma yanzu da na zama Madaki sai ayyuka suka karu gare ni. Ka ga bayan gudanar da shari’a ko in ce sulhu a tsakanin al’ummar Lafiya da kewayenta, na kuma kasance babban mai ba Mai martaba Sarkin Lafiya shawara ta musamman a kan harkokin dukan hakimai da ke masarautar nan. Kowane hakimi da ke da damuwa ko yake so ya ga Sarki dole ne ya biyo ta wurina don ni ne kawai zan iya sada shi da Sarki. Idan kuma damuwarsa wadda zan iya magance ta ce to, nakan yi haka ba ma sai ya kai ga Mai martaba ba. A takaice dai bambancin shi ne yanzu ayyuka sun karu min fiya da yadda suke a da. Amma da ikon Allah kuma da yake na riga na saba da aikin sai ya kasance ba na fuskantar matsala wajen gudanar da wadannan ayukana. A bangaren aikin gwamnati da na yi a da kuma shi ne shi aikin gwamnati kamar yadda ka sani akwai iko. Da nakan iya yi amfani da ikona in umarci dan sanda ya je ya kama wani a hukunta shi idan ya aikata laifi. Amma yau ba na iya yin haka. Ina sasanta mutane ne da suke rikici. Duk abin da ya faru nakan zauna ne in sasanta su. Don mutane sun san amfanina. Shi ya sa sau da yawa maimakon mutum ya tafi kotu sai ya zo wurina ni kuma in sasanta su. Amma fa ba dole ba ne mutum ya zo wurina sai ya ga dama. Kuma da yawa yanzu sun gane cewa zuwa wurinmu ya fi amfani fiye da tafiya kotu don za a fi yin musu adalci a wurinmu. Don idan kana da gaskiya za mu fada maka kuma idan ba ka da gaskiya za mu fada maka komai girman matsayinka.
Wasu jihohin Arewa suna hana barace-barace, ko kuna da niyyar yin haka a masarautar nan?
Maganar barace-barace dai ka ga ba mu muka kawo ba, babu masu bara a jihar nan. Amma kamar yadda ka bayyana ne akwai wasu jihohin Arewa sun hana barace-barace kuma ana samun tashin-tashina a wadannan jihohi. Mu kuma da yake muna zaman lafiya a nan sai wadannan masu bara suna ta zuwa nan. Amma a yanzu ba zan iya ce maka ga abin da za mu yi game da haka ba. Domin zuwan bako a kasa arziki ne. Kodayake barace-baracen nan ba abin alheri ba ne. Amma ba ma so mu dauki wani mataki cikin gaggawa game da lamarin don baki ne dole ne mu bi komai a hankali. Wasu wurare ana sa su a mota ne kawai kowa ya koma inda ya fito. Watakilla gwamnati ta iya yin haka amma mukan ba za mu iya yin haka ba, don muna ganin bai dace ba. Saboda dukanmu ’yan Najeriya ne kuma karfinmu ba daidai ba ne.
Kwanakin baya Mai martaba Sarkin Lafiya ya yi bikin cika shekara 40 a kujerar sarauta. Wane ci gaba aka samu a wadannan shekaru?
A gaskiya an cimma nasarori da dama a jihar nan baki daya cikin wadannan shekara 40 a karkashin jagorancin Mai martaba Sarkin Lafiya. Domin idan ka lura Sarkin Lafiya shi ne shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta jihar nan baki daya. Saboda haka ayyukansa suna shafar kowace masarauta da yankunan jihar nan. Shi ya fafata har aka ba Lafiya fadar jihar nan wadda a da fadar karamar Hukumar Lafiya ne kawai. Ba ya zama yau yana nan gobe yana can. Ba ya gajiya idan da wani abu da ya kamata ya samu Shugaban kasa yana tafiya Abuja da kansa ya same shi ba tare da bata lokaci ba, ya ce masa ga abin da yake so a kawo jiharsa, saboda haka idan zan bayyana maka abubuwan ci gaba da Mai martaba Sarki Isah Mustapha Agwai ya kawo jihar nan da kasa baki daya a cikin shekara 40 sai mu dauki dogon lokaci. Manyan makarantu ne ga jihar nan shi ya fafata aka kirkiro ta a 1996. Shi ya sa mu a kullum addu’armu ita ce Allah Ya ja zamaninsa Ya kuma kara masa lafiya, don mu ci gaba da cin moriyarsa a jihar nan baki daya. Domin a gaskiya rashinsa zai ba mu wahala sosai ba, a nan masarautar Lafiya kawai ba har ma da jihar nan baki daya.
To, yallabai a karshe batun yunkurin tsige Gwamna Al-Makura, ko kana da wata shawara ga ’yan Majalisar Dokoki da bangaren Zartarwar jihar?
Ni dai roko nake yi a gare su ba maso a danne hakkin wani. Da su da gwamnati da bangaren shari’a kowa na da nasa aiki. Saboda haka kowa ya tsaya ga nasa aiki a daina shiga na wani. Mu dai iyayensu ne dukkansu ba za mu tashi muna goyon bayan wani ba. Sai dai mu roke su, su sasanta takaddamar da ke tsakaninsu, mu kuma mu yi musu addu’a. Shi Gwamna abin da ’yan majalisar ke nema a wurinsa idan bai fi karfinsa ba ya ba su. Su kuma ’yan majalisa idan an samu rashin jituwa irin wannan su daina garajen cewa a yi canji, a yi canji, domin ba a san halin wanda ake so a kawo ba. Gwamna Al-Makura ya san matsalar talakawan jihar nan ba ra’ayi ba. A karshe kada mu manta cewa dukkanmu ’yan uwan juna ne mu daina sauraren wasu mutane daga waje da ke sa mana baki a harkokin jiharmu don bata mana sha’ani.