✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An samu ci gaba a bangaren wasanni a Nasarawa – Kwamishina

A tattaunawar da wakilinmu ya yi da Kwamishinan Matasa da Wasannin na Jihar Nasarawa, Malam Ishak Ahmad Galadima a Lafiya, ya bayyana yadda aka samu…

A tattaunawar da wakilinmu ya yi da Kwamishinan Matasa da Wasannin na Jihar Nasarawa, Malam Ishak Ahmad Galadima a Lafiya, ya bayyana yadda aka samu ci gaba a bangaren wasanni a karkashin gwamnatin Umaru Al-Makura:

Aminiya: Wane ci gaba aka samu a bangaren wasanni a gwamnatin Al-Makura?
Kwamishina: Gaskiya a wannan gwamnati na Mai girma Gwamnan Jihar Nasarawa, Umaru Tanko Al-Makura an samu ci gaba da dama kamar gyara babban filin wasa na Lafiya, inda aka gyara wurin zaman manyan baki aka kuma kawata shi. Kuma a zamaninsa ne kungiyar kwallon kafa ta Jihar Nasarawa wato Nasarawa united ta samu nasarar wakiltar Najeriya a kasar kasashen Afirka.
Aminiya: Ta yaya Nasarawa United ta samu nasarar wakiltar Najeriya a gasar kasashen Afirka?
Kwamishina: Ta samu nasarar ce sakamakon nasara da tayi a wasan rukunin Firimiya inda ta zo ta uku, hakan ya ba ta dama ta wakilci Najeriya a wasan da ake kira Confederation Cup wato Kofin kalubale. Wannan wasa ana yi a gida da waje, mun yi da kasar Senegal da wata kungiyar Generation Foot, ta zo nan Najeriya muka buga muka doke ta, muka sake bin ta gidanta a Senegal a garin Dakar inda muka yi canjaras. Shi ya ba kungiyarmu damar zuwa zagaye na biyu. Wannan kuma mun yi da kasar Aljeriya ce da wata kungiya da ke Kostantin, sun zo mun doke su da muka bi su gidan su sai suka doke mu. To wannan ne dalilin da ya sa Nasarawa United ba ta ci gaba a wasan ba, amma ko ba komai mun yi kokari fiye wasu kungiyoyin kwallon kafa na wasu jihohi. Kuma kasancewar Jihar Nasarawa karamar jiha ce, amma ta wakilci Najeriya a waje, wannan abin alfahari ne kwarai da gaske. Haka ma akwai kungiyar kwallon kafa ta mata wanda ake kira Nasarawa Amazon wanda suna yin iya bakin kokarinsu.
Aminiya: Ko akwai abin da kake zargin ya jawo faduwarku a wasan?
Kwamishina: Ka san nasara da rashin nasara duk daga Allah ne, amma gaskiya wasa na bukatar dage damtse. Kuma wanda ya yi nasara ya daina ganin koyaushe zai samu nasara, domin babu mamaki na gaba ya koma baya, wadansu ’yan wasa da zarar sun ga suna doke kungiyoyi sai su fara zaton babu mai doke su. Wannan na daya daga cikin dalilin da ya kayar da mu a wasan. Kodayake ina jinjina wa kungiyar kwallon kafa ta mata da ta maza ta Jihar Nasarawa domin suna matukar kokari
Aminiya: Wadansu na tunanin wasa sana’a ce da matashi ke wahala kafin ya ci moriyarta, me za ka iya cewa game da hakan?
Kwamishina: A’a ba haka ba ne, kuma ina kira ga matasa su kasance masu son harkokin wasanni, domin wasanni suna da matukar fa’ida ga matasa saboda suna sanya nishadi da motsa jiki kuma suna iya zamo wa mutum abin dogaro. Domin a wannan lokacin, babu sana’a mai saurin kawo kudi kamar wasanni musamman kwallon kafa wadda yanzu haka muna da ’yan Jihar Nasarawa da dama da suke ci suke sha a harkar wasanni. Kuma ba ya ga kasancewa dan kwallon kafa, akwai abu mai matukar amfani a harkar wasannin da ake samun alheri mai yawa a cikinsa, wato kamar aikin hura wasa da horar da ’yan wasa. Don haka ina shawartar matasa su kasance masu koyon wadannan ayyuka biyu, sa’annan su kasance masu neman abin kansu domin dogaro da kansu su daina dogara kacokan kan gwamnati.
Aminiya: Ta yaya kuke zakulo matasa zuwa kungiyar Nasarawa United?
Kwamishina: Muna samun matasa ne ta hanyar gwaje-gwajen da muke musu tun daga kauyukansu, inda a nan ne muke iya zabo hazikan ’yan wasan kwallon kafa.