✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An samar da takalmin da zai hana makafi fadawa hadari

Ruwa ba zai lalata takalmin ba, wanda kudinsa ya haura naira miliyan daya.

Wani kamfani a Austireliya mai suna Tec-Innovation ya gabatar da wasu takalma masu amfani da na’urori da auna sigina don taimaka wa makafin da ba sa iya hango nesa don taimaka masu wajen gano wurare masu hadari a tsawon mita hudu.

Wannan takalmi da kamfanin ya sa masa suna InnoMake, zai maye gurbin amfani da sanda da miliyoyin mutane a duniya ke dogaro da ita don tafiya a shekaru da dama.

Samfurin da ake da shi a halin yanzu ya dogara da na’urori masu gano matsaloli wajen tafiya kuma tana fadakarwa ta hanyar wata manhaja a cikin wayoyin hannu masu hade da Bluetooth.

Kamfanin ya riga ya fara aiki da ingantaccen tsarin da ya kunshi kyamarori da kwarewar fasaha ba kawai don gano matsaloli ko hadari ba har ma da yanayi su.

Tec-Innovation ya hada hannu da Jami’ar Kere-Kere ta Graz ta Austireliya don habaka ingantaccen tsarin ilimin kerekere na zamani da aka tsara kan hanyoyin Intanet.

Za su yi nazarin bayanan da na’urori masu auna sigina da kyamarorin da aka saka a cikin takalmin InnoMake suka bayarwa don tantance ko hanyar da ake tafiya da takalmin ba ta da matsala, da kuma rarrabe tsakanin nau’o’in matsalolin hanyar da ake bi da takalmin.

“Ba kawai na’urar za ta nuna alamar gargadi ba ne game da fuskantar wata matsala da zaa iya cin karo da ita, har ma da bayanin irin matsalar da za a iya fuskanta.

Domin tana da babban bambanci gano cin karo da bango ko mota ko matakala ce,” inji Markus Raffer daya daga cikin wadanda suka kafa Kamfanin Tec-Innobation, ya bayyana wa TechDplore.

“Na’urori masu auna sigina a kafar da aka sanya wa takalmin zai iya gano wasu matsaloli da za a iya cin karo da su tsawon mitahudu, wanda ya sanya takalmin zai ji motsin na’urar.

Kudin takalmin ya haura Naira miliyan daya da rabi

Wannan na’urar na aiki kamar yadda ake bukata, har ta taimaka min ni kaina,” inji Raffer wanda shi yake da nakasa.

A yanzu haka takalmin na InnoMake yana kasuwa kuma za a iya sayensa a shafin Intanet na Tec-Innovation kan Dala 3,850 (daidai da Naira miliyan 1 da dubu 568 da da dubu 568 da 836 da kwabo 50), ba tare da aikin kyamarar ba wadda ba a kammala ba.

Idan aka mallaki takalmin yana da na’urar da za ta iya tattara bayanai na muhallin da yake da kuma inda aka yi yawo da takalmin.

Ruwa ba zai lalata takalmin ba, haka kura ba ta yi masa illa kuma sannan yana dauke da batiri mai inganci da zai iya aiki da na’urori na tsawan mako guda kuma za a iya cajin batirin ya cika.