Gwamna Neja, Abubakar Sani Bello, ya sallami Kwamishinan Ayyuka da Kyautata Rayuwa na Jihar, Injiniya Ibrahim Mohammed Panti.
Sakatariyar Yada Labaran Gwamnan, Mary Noel-Berje, ta ce sallamar Kwamishinan wanda kuma shi ne Shugaban Kwamitin Albashi na Jihar, ta fara aiki ne nan take, amma ba ta bayyana dalilin sallamar ba.
Sanarwarta kara da cewa Kwamishinan Tsare-tsaren Jihar, Mamman Musa zai maye gurbin Injiniya Ibrahim, a yayin da Kwamishinan Kudi, Zakari Abubakar zai zama mai kula da Ma’aikatar Tsare-tsare a kan aikinsa.
“Mamman Musa zai mika Ma’aikatar Tsare-tsare ga Zakari shi kuma Injiniya Ibrahim Mohammad Panti zai mika wa Mamman Musa nan take,” inji sanarwar da ta fitar.