An sako Sarkin Bungudu, Alhaji Hassan Attahiru, bayan shafe wata daya a hannun ’yan bindiga da suka yi garkuwa da shi.
Wata majiyar tsaro ta ce an sako Sarkin Bungudu ne a yammacin ranar Asabar a Jihar Kaduna, wata guda bayan ’yan bindiga sun bude wa ayarin motocinsa wuta sannan suka yi awon gaba da shi a kan hayar Abuja zuwa Kaduna.
- Na sa an sace babana an kashe shi, aka ba ni N2,000 —Dan bindiga
- EFCC ta titsiye Kwankwaso kan badakalar kudaden fansho
Da yake tabbatar da labarin sako basaraken, Mashawarcin Gwamnan Jihar Zamfara kan Dabaru, Gazali Shehu Ahmad, ya ce, “A madadin iyalai da Masarautar Bungudu, muna mika godiyarmu ga al’umma bisa irin addu’o’i da goyon bayan da suka ba mu a tsawon lokacin da wannan ibtila’i ya same mu.
“Muna godiya ga Gwamnatin Jihar Kaduna bisa kokarin da ta yi a tsawon wannan lokaci; Hakazalika Gwamnatin Jihar Zamfara da ta taka muhimmiyar rawa domin ganin uban kasarmu ya dawo cikin koshin lafiya,” kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Sanarwar ta yi “Godiya ta musamman ga Rundunar ’Yan Sandan Najeriya da Kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah bisa gudummawar da suka bayar wajen ganin an sako sarkin,” sannan ta kara da cewa sarkin zai shafe makonni masu zuwa yana duba lafiyarsa.
Idan ba a manta a baya Aminiya ta kawo rahoton yadda masu garkuwa da sarkin Bungudun suka karbi kudin fansar Basaraken Naira miliyan 20 amma suka ki su sako shi da cewa sai an kara musu.
An yi garkuwa da basaraken ne bayan ’yan bindiga sun bude wuta a kan ayarin motocinsa da wasu motocin haya a ranar 14 ga watan Satumba, 2021.
Lamarin ya ritsa da shi da fasinjojin motocin hayan ne a daidai kauyen Dutse, lokacin yake kan hanyarsa ta zuwa Gusau, gabanin tafiya domin halartar Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York na kasar Amurka.