Rundunar ‘yan sandan jihar Bayelsa ta tabbatar da sakin mahaifiyar Tsohon Kocin Kungiyar Kwallon Kafa ta Kasa Samson Siasia, mai suna Misis Ogere Beuty Siasia, mai shekara 79.
An sace Misis Ogere, tun ranar 15 ga watan Yuli bana a gidanta da ke Odini, a Karamar Hukumar Sagbama a Jihar Bayelsa.
A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar , SP Asinim Butswat ya fitar na cewa, a yanzu haka Kwamishinan ‘yan sandan jihar ya ziyarci Misis Ogere, bayan an kubutar da ita a yau Lahadi.