Mahukuntan kasar Habasha sun sako jagoran ’yan adawan kasar, Mista Merera Gudina bayan ya shafe sama da shekara daya a tsare a kurkuku.
Jami’an kurkuku sun shaida wa iyalansa cewa an sako shi a shekaranjiya Laraba da safe inda aka bar shi ya koma gidansa.
Mista Gudina yana tsare ne a kurkuku tun watan Disamban shekarar 2016, inda ake zarginsa da aikata ayyuka da dama ciki har da alaka da kungiyoyin ’yan ta’adda.
Gwamnatin Habasha ta fadi a ranar Litinin da ta gabata cewa za ta janye tuhume-tuhumen da take ga sama da mutum 500 da ake zargi da aikata ba daidai ba.
A farkon wannan wata ne gwamnatin ta ce za ta yi afuwa tare da janye wasu shari’u da aka yi wa ’yan siyasa da dama da wadanda shari’unsu suke gaban kotuna a wani yunkuri na karfafa hadin kan kasa.
Sanawar ta biyo bayan sama da shekara biyu ana gudanar da bore don nuna adawa da gwamnati, inda masu zanga-zanga suka rika kiraye-kiraye a sake fasalin harkokin siyasa da na tattalin arziki tare da kako karshen almundahana a tsakanin jami’an gwamnatin da kuma daina cin zarafin dan Adam.
Gwamnatin Habasha dai ta sha musanta cewa akwai fursunonin siyasa a kasar, kamar yadda kungiyoyin kare hakkin jama’a da ’yan adawa suke zargi.