Wani kamfanin kasar China ya sanar da sakin ɗaya daga cikin jiragen Shugaban Nijeriya da yake riƙe da su.
Aminiya ta ruwaito cewa kamfanin mai suna Zhongshan Fucheng Industrial Investment Company Limited yana riƙe da jiragen ne bisa halascin wata kotun Faransa a filayen jirgin sama na Paris-Le Bourget da Basel-Mulhouse.
Jiragen da kamfanin yake riƙe da su na Fadar Shugaban Nijeriyar sun hada da Dassault Falcon 7X, da Boeing 737-7N6/BBJ da kuma Airbus A330-243.
Dalilin da aka riƙe jiragen
Tun farko kamfanin ya buƙaci wata kotu a Faransa ta ba shi damar ƙwace wasu kadarorin Gwamnatin Najeriya da darajarsu ta kai ta kuɗi fam miliyan 74.5 da ke ƙasashe takwas na duniya.
Kamfanin Zhongshan Fucheng Industrial Investment Company Limited ne ya nemi buƙatar hakan domin samun diyya kan wata rigimar kwangila da ta shiga tsakaninsa da Gwamnatin Jihar Ogun tun a shekarar 2016.
A shekarar 2016 ce kamfanin na Zhongshan ya shigar da ƙara, bayan da Gwamnatin Jihar Ogun ta soke kwangilar da suka cimma da wani reshen kamfanin mai suna Zhongfu a 2013 na samar da wasu kamfanonin kasuwanci masu sauƙin haraji a jihar.
Yunƙurin kamfanin na sake farfaɗo da yarjejeniyar ya gamu da cikas a 2018 lokacin da kamfanin ya garzaya wasu kotunan ƙasar da buƙatar farfaɗo da yarjejeniyar.
To amma a watan Maris ɗin 2021, wata kotu ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙotun Ƙolin Birtnaiya, ta yanke hukuncin cewa gwamnatin jihar ta biya kamfanin diyyar Dala miliyan 74.5 , amma sai Gwamnatin Jihar Ogun ta yi biris da hukuncin.
‘Dalilin da muka saki jirgin’
Sai dai a cewar mai magana da yawun kamfanin, an saki daya daga cikin jiragen bayan an sanar da su cewa Shugaban Nijeriya Bola Tinubu zai bukaci amfani da jirgin ne domin ziyarar da zai kai wa Shugaban Faransa, Emmanuel Macron.
Cikin sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Juma’a, “Zhongshan ya ci gaba da dawainiyar lamarin bisa gaskiya da adalci a yayin takaddamar shari’a da Najeriya.
“Muna sanar da cewa mun saki jirgin Airbus A330, wanda a halin yanzu yake tsare a kasar Faransa, sakamakon umarnin kotun Faransa da Zhongshan ya samu.
“Umarnin ya nuna cewa ana bukatar jirgin saboda Shugaban Nijeriya zai yi jigila da shi zuwa wata ganawa da Shugaba Emmanuel Macron na Faransa a farkon mako mai zuwa.
“Saboda mutuntawa da karamci, Zhongshan ya saki jirgin nan take. Hakan zai bai wa Shugaba Nijeriyar damar yin amfani da shi wajen tafiyar.”
Kakakin ya bayyana cewa, kamfanin zai ci gaba da jajircewa wajen tattaunawa da Gwamnatin Nijeriya da nufin cimma matsaya mai ma’ana.