✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An saki mataimakin kwamishinan ’yan sandan da aka sace a Kaduna

An saki Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda, ACP Emmanuel Agene wanda aka sace a ranar Larabar da ta gabata yayin da yake balaguro zuwa jihar Zamfara…

An saki Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda, ACP Emmanuel Agene wanda aka sace a ranar Larabar da ta gabata yayin da yake balaguro zuwa jihar Zamfara tare da direbansa.
Mataimakin Kwamishanan ’Yan sandan tare da direbansa suna cikin koshin lafiya a yammacin ranar Asabar din da ta gabata kuma suna hannun rundunar ’yan sanda ta jihar Kaduna.
Rundunar ’yan sanda ta tsananta bincike a kan hanyar Birnin Gwari zuwa garin Futuwa tun lokacin da suka sami labarin sace mataimakin kwamishinan ’yan sandan kuma suka sami nasarar gano inda tsare shi tare da direbansa.
Wadanda suka sace shi sun gudu sun bar mataimakin kwamishinana ’yan sandan tare da direbansa  yayin da suka gano cewa an gano maboyarsu ta jirgi mai sarrafa kansa da ke shawagi a yankin.