Gwamnatin Kano ta ba da umarnin rufe dukkan gidajen kallo da wuraren taruka da bukukuwa a fadin Jihar a wani matakin na dakile yaduwar cutar COVID-19 a karo na biyu.
Kazalika, gwamnatin ta kuma umarci dukkan ma’aikatanta da su zauna a gida har zuwa lokacin da za ta bayar da umarni na gaba.
- Yadda gwamnoni ke facaka da biliyoyin Naira a zaben kananan hukumomi
- ’Yan sanda sun cafke mace mai garkuwa da mutane a Kano
Umarnin na kunshe ne a sanarwar da Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar, Malam Muhammad Garba ya raba wa ‘yan jarida da sanyin safiyar ranar Talata a Kano.
Ya ce daukar matakan na daga cikin shawarwarin taron da masu ruwa da tsaki suka gudanar a jihar ranar Litinin.
Ya ce, “Ma’aikata masu ayyuka na musamman kamar jami’an lafiya, ‘yan kwana-kwana, ma’aikatan ruwa, malamai, jami’an tsaro da kuma kafafen watsa labarai wannan umarnin bai shafe su ba.”
Malam Muhammad Garba ya kuma sake jaddada aniyar Gwamnatin Jihar na aiki kafada-da-kafada da malaman addini da sauran masu ruwa da tsaki a jihar wajen tabbatar da cewa jama’a na bin matakan kariya daga cutar.
Daga nan sai ya ja kunnen jami’an tsaro kan su tabbatar an bi umarnin, yana mai cewa ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen hukunta masu kunnen kashi.
Sai dai umarnin gwamnatin na zuwa ne sa’o’i 24 bayan sake bude makarantu a jihar, duk kuwa da barazanar ci gaba da yaduwar cutar.
Wannan ne dai karo na biyu da jihar ta bayar da irin wannan umarnin tun bayan barkewar cutar COVID-19 a farkon 2020.