✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An sake rage farashin man fetur a Najeriya

Hukumar kula da farashin albarkatun man fetur ta Najeriya PPPRA ta sake rage farashin litar man fetur daga Naira 125 zuwa Naira 123.5. A wata…

Hukumar kula da farashin albarkatun man fetur ta Najeriya PPPRA ta sake rage farashin litar man fetur daga Naira 125 zuwa Naira 123.5.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar a Abuja, hukumar ta shaida cewa an rage farashin ya ne biyo bayan amincewar gwamnatin tarayya na rage farashin zuwa Naira 123.5 wanda zai fara aiki daga yau, 1 ga watan Afrilu.

A karo na biyu kenan da mahukuntan gwamnatin Najeriya suka rage farashin man fetur tun bayan barkewar annobar Coronavirus lamarin da ya sanya farashin danyan man fetur faduwa warwas abin da ba a taba gani ba cikin shekaru 18 da suka gaba ta inda zuwa yanzu farashin gaggan man fetur ya koma dalar Amurka 22 a kasuwannin duniya.

A cewar sanarwar, an rage farashin ne bisa la’akari da yadda farashin danyen mai ya fadi a kasuwannin duniya sakamakon cutar coronavirus.

Farashin danyen man fetur ya yi mummunar faduwar da bai taba yin irinta ba cikin shekaru da dama a kasuwannin duniya.

Barkewar cutar Coronavirus a duniya ya shafi yadda ake sayen man a kasuwar duniya.